A yayin ziyarar da ya kai kasar Kenya a ranar Litinin, mista Kerry ya tattauna da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, bayan hakan, ya sadu da ministocin kasashen Afrika ta gabas wadanda suka hada da Kenya, da Uganda, da Somaliya, da Sudan da Sudan ta kuda, inda suka tattauna game da tashe tashen hankalin da suka barke a Sudan ta Kudu. A wani zaman taron 'yan jarida da ta kirawo bayan sun kammala tattaunawa da mista Kerry, ministan harkokin kasashen wajen ta Kenya Mrs Amina Mohamed ta bayyana cewa, tuni shugabanin sojojin kasashen Afrika ta gabas suka tattauna wajen neman hanyoyin nagari domin aika sojojin kariya kamar mutane dubu 4 a Sudan ta Kudu. Mrs Amina Mohamed ta kara da cewa, wadannan sojojin da za'a aika cikin gaggawa za su kasance karkashin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD.
A farkon watan Yuli, tashe tashen hankali sun sake barkewa tsakanin bangarorin kasar biyu masu gaba da juna, inda ake tsoron fadawar kasar cikin wasu sabbin tashe tashen hankula. Kungiyoyin biyu na Sudan ta Kudu masu gaba da juna sun jefa kasar cikin yakin basasa a shekarar ta 2013. Duk da cewa a watan Agusta na shekarar bara bangarorin biyu sun rattaba wata yarjejeniyar zaman lafiya, wadda ba ta hana kasar kasancewa ba cikin wadannan su sabbin tashe tashen hankali. A dalilin haka Kungiyar hadin kan gwamnatoci domin ci gaba (IGAD), wadda ta hada da gungu kasashen Afrika ta gabas, sun ba da shawarar aika sojojin kare zaman lafiya a kasar, a lokacin da tashe tashen hankali suka sake barkewa a Sudan ta Kudu, AU da kwamitin tsaro na MDD sun bada amincewar aika sojojin kariya. A farko shawarar gwamnatin Sudan ta Kudu ta nuna rashin amincewarta wajen ganin an aika sojojin cikin kasarta, inda a karshe ta amince. Mista Kerry ya shaida cewa wadannan sojojin kariyar, ba za su yi amfani da karfi ba, aika su shi ne kare fararen hula da hare hare, da kuma ba su damar yin zirga zirga cikin lumana. (Laouali Souleymane)