Kungiyar adawa da jam'iyyar SPLM ta bayyana jiya Alhamis cewa, tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta kudu Riek Machar ya fice daga kasar, kuma yanzu haka yana zaune a wata kasa da ke makwabtaka da kasar da aka yi imanin cewa za ta kare lafiyarsa.
Ram Chalk wakilin gudanarwa na kungiyar adawar nan dake kasar Kenya, ya shedawa manema labaru cewa, a ranar Talata ce Riek Machar ya bar Sudan ta kudu saboda wasu dalilai na tsaro, amma bai fayyace kasar da Riek Machar ya ke ba.
Ram Chalk ya bayyana cewa, Riek Machar dai ya fara fuskantar barazanar tsaro ne tun lokacin da rikici ya barke a Sudan ta kudu a farkon watan Yuli. (Amina)