in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan da Sudan ta kudu zasu maido tattaunawa game da shata kan iyakoki
2016-08-28 14:25:09 cri
Cibiyar yada labaran kasar Sudan ta rawaito cewa a jiya Asabar, kasashen Sudan da Sudan ta kudu suka amince su dawo da tattaunawa game da batun shata kan iyakokin kasashen biyu wanda ake saran gudanarwa a watan Satumba.

A watan Yunin wannan shekara ne aka amince da cigaba da tattaunawa tsakanin kasashen biyu game da batun, sai dai ana samun jinkiri ne a lokuta da dama, a sakamakon tabarbarewar al'amurran tsaro da Sudan ta kudun ke fuskanta.

Jakadan Sudan ta kudu ya fada cewa, kasar sa ta amince a lokacin da aka tsai da na aiwatar da yarjejeniyoyi 9 da aka cimma game da shata kan iyakokin kasashen biyu.

Yace gwamnatin Sudan ta kudu ta amince ta aiwatar da yarjejeniyoyin a zahiri, ta hanyar janyewa dakarun daga nisan kilomita 10 a cikin kasarta, wanda MDD ta tsara hakan.

A watan Satumbar 2012, kasashen Sudan da Sudan ta kudu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar, wadanda suka hada da yarjejeniyoyi 9 da suka shafi kasashen biyu, wanda aka amince dasu a Addis Ababa na kasar Habasha karkashin kulawar kungiyar tarayyar Afrika AU.

To sai dai , wadan nan yarjejeniyoyin basu warware batutun shata kan iyakokin Abyei da na shata iyaka ba.

Batun kan iyakoki na daya daga cikin babbar matsalar dake haifar da tada jijiyar wuya tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu, wanda ya hada da rikici kan iyakokin yankuna 5, da suka hada da; Abyei, da Dabatal-Fakhar, da Jabel Al-Migainis, da Samaha da kuma Kafia Kanji.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China