Tun a watan Maris na bana ne, gwamnatin kasar Sudan da jam'iyyun adawa na kasar da dama suka daddale yarjejeniyar taswirar shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, karkashin kulawar kungiyar tarayyar Afirka.
Dangane da lamarin, Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Alhamis a nan Beijing cewa, kasar Sin na mara wa Sudan baya wajen kiyaye 'yancinta da na yankunanta. A saboda haka, tana kira ga sassa daban daban masu ruwa da tsaki da su aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, ta hanyar shiga shirin yin tattaunawa a tsakanin al'ummar kasar cikin hanzari, a kokarin ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar ta Sudan baki daya. (Tasallah Yuan)