Gwamnatin lardin Guangdong, bankin raya kasa na kasar Sin da kuma bankin duniya ne suka shirya wannan taro cikin hadin gwiwa, bisa taken "yin musayar fasahohin neman bunkasuwa, domin inganta hadin gwiwar Sin da Afirka", haka kuma, a yayin taron manema labarai da aka kira a jiya Litinin dangane da wannan taro, mataimakin babban sakataren gwamnatin lardin Guangdong Zhang Aijun ya bayyana cewa, yanzu, an tabbatar da cewa,ministocin kasashen Afirka sama da 20 ne za su halarci taron, kuma an shirya tsaf don gudanar da wannan taron cikin nasara.
Hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakanin lardin Guangdong da kasashen Afirka tana bunkasa cikin sauri, musamman ma a tsakanin shekarar 2003 zuwa shekarar 2015, darajar cinikayya dake tsakanin lardin Guangzhou da Afirka ta karu daga dallar Amurka biliyan 2.8 zuwa dallar Amurka biliyan 43.1, adadin da ya ninka har sau 14. A halin yanzu kuma, nahiyar Afirka ta kasance daya daga cikin manyan abokan cinikayya guda 10 na lardin Guangdong. (Maryam)