Shugaban kungiyar kula da harkokin diplomasiya ta Sin, Li Zhaoxing ya bayyana a gun dandalin tattaunawar cewa, an sami babbar nasara a gun taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka da aka gudanar a watan Disamban bara. Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, kawo yanzu baki daya yawan yarjeniyoyin da aka daddale ya kai sama da 240, yayin da jimillarsu ta kai sama da dala biliyan 50.
Wakilai daga sassan siyasa da masana'antu da na kafofin yada labarai da yawa dake halartar taron sun bayyana cewa, yin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka ba ma kawai na bukatar tattara jari ba, har ma ana bukatar tattara hikima.
Shugaban kwalejin nazarin harkokin watsa labarai na jami'ar Renmin ta Sin, kana tsohon darektan ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa, Zhao Qizheng ya ba da shawara cewa, kamata ya yi kafofin yada labarai na Sin da na kasashen Afirka su yi amfani da wannan zarafi na yin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, su sami ci gaba tare, su sami moriyar tare, kuma su dora muhimmanci kan watsa labarai daga dukkan fannoni a yayin da ake yada fasahohin da Sin da kasashen Afirka suka samu daga wajen junansu.
Ministan sufuri da manyan ayyuka na Kenya, James Macharia ya gabatar da jerin ayyukan da ake yi da kuma za a yi bisa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, kamar hanyar jirgin kasa da ta hada Mombasa da Nairobi da sauransu. Ya ce, ana yin hakikanin hadin gwiwa tsakanin Sin da Kenya bisa bukatun gaggawa.(Fatima)