An kaddamar da shagalin matasan Sin da Afirka na shekarar 2016 a birnin Guangzhou na kasar Sin
A yau ne aka kaddamar da shagalin kwanaki hudu na matasan Sin da Afirka na shekarar 2016 a birnin Guangzhou na kasar Sin, inda mataimakin gwamnan lardin Guangdong He Zhongyou, mataimakiyar shugabar kungiyar sada zumunta ta kasashen waje ta kasar Sin Lin Yi, shugabar tawagar jakadun kasashen Afirka dake kasar Sin kuma jakadan kasar Madagascar Victor Sikonina suka halarci bikin bude shagalin tare da yin jawabai.
Shagalin wani bangare ne na aiwatar da shirin kai ziyara ga juna a tsakanin matasan Sin da Afirka da aka cimma a taro kolin Johannesburg na FOCAC da aka gudanar a watan Disamba na shekarar bara. Wakilai 200 daga kasashen Afirka 18 ne suke halartar shagalin, inda ake sa ran za su yi musayar ra'ayoyi da takwarorinsu dake lardin Guangdong a fannonin tattalin arziki, cinikayya, al'adu, hidimar zamantakewar al'umma da dai sauransu. (Zainab)