Darektan kula da harkokin siyasa a ma'aikatar harkokin wajen kasar Togo Dr. Bakayota Koffi Kpaye shi ne ya bayyana hakan a jiya Talata yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin.
A yau Laraba da kuma gobe Alhamis za a fara tattauna a Lome kamar yadda cibiyar Cater ta tsara, gabanin taron kolin kungiyar tarayyar Afirka kan tsaro da ci gaban harkokin teku a Afirka da za a gudanar a watan Oktoba.(Ibrahim)