in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar kasuwanci ta Sin: Sin za ta kara taimakawa kasashen Afirka
2016-07-26 17:12:30 cri
A ranar 29 ga wata, za a gudanar da taron masu kula da aikin aiwatar da yarjeniyoyin da aka kulla a taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a birnin Beijing na Sin. A yau Talata 26 ga wata, jami'a mai kula da harkokin kasuwanci ta hukumar yammacin Asiya da Afirka ta ma'aikatar kasuwanci ta Sin, madam Shu Luomei ta bayyana cewa, tallafin da kasar Sin take baiwa kasashen Afirka bai wuce karfinta ba, don haka kasar za ta kara taimakawa kasashen Afirka bisa karuwar karfin tattalin arzikinta.

An ba da labarin cewa, yanzu Sin tana gudanar da ayyukan ba da tallafi a wasu kasashe sama da 50 dake nahiyar Afirka, tare da gina hanyoyin jirgin kasa da tsawonsu ya kai sama da kilomita 2000, da hanyoyin mota da tsawonsu ya kai sama da kilomita 3000, da makarantu sama da 100, da asibitoci 60 a kasashen Afirka, kuma ta yafe wa kasashen Afirka bashi da yawansa ya kai sama da kudin RMB biliyan 10.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China