A yayin ganawar tasu a na birnin Beijing, Li Yuanchao ya ce, an cimma nasarar taron FOCAC da ya gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a shekarar da ta gabata, inda aka bude wani sabon babin hadin gwiwar Sin da Afirka iri na cimma moriyar juna da kuma neman bunkasuwa cikin hadin gwiwa.
A saboda haka, ya ce ana fatan Sin da Afirka za su karfafa fahimtar juna dake tsakaninsu, haka kuma za su ci gaba da inganta hadin gwiwarsu yadda ya kamata, a yayin da ake aiwatar da sakamakon taron na FOCAC. (Maryam)