in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matsayin kasar Sin ta fuskar ciniki da kasashen Afirka yana kyautatuwa
2016-08-23 20:52:48 cri

A yau Talata ne, kwalejin nazarin kimiyyar zamantakewar al'ummar kasar Sin ya kaddamar da takardar bayani dangane da nahiyar Afirka, inda ya ce, ko da yake sha'anin fitar da kayayyaki na kasashen Afirka zuwa kasashen ketare bai inganta kamar yadda na sauran kasashen duniya ba, duk da haka matsayin kasar Sin ta fuskar yin cinikayya da kasashen Afirka yana kyautatuwa. A shekarar 2015, yawan kudaden da kasar Sin ta samu daga fitar da kayayyaki zuwa kasashen Afirka ya karu zuwa 4.7 cikin 100 bisa jimilar kudaden da kasar Sin ta samu daga fitar da kayayyaki zuwa ketare, yayin da yawan kudaden da Sin ta kashe wajen shigo da kayayyaki daga Afirka ya ragu zuwa 4.1ciki 100 bisa jimilar kudaden da ta kashe wajen shigo da kayayyaki daga ketare.

Takardar bayanin ya yi nuni da cewa, a shekarun baya, sakamakon manufar habaka ciniki a kasashen ketare da kasar Sin take aiwatarwa, ya sa kasar Sin ta kara zuba dimbin jari a kasashen Afirka. Ko da yake kasar Sin ta fuskanci kalubale wajen zuba jari a Afirka, amma kasashen Sin da Afirka sun aza harsashi mai kyau wajen yin hadin gwiwa a tsakaninsu, kuma suna da kyakkyawan burin ci gaba da yin hadin gwiwa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China