Za a gudanar da taron kolin G20 karo na 11 a birnin Hangzhou na kasar Sin tun daga ranar 4 ga watan Satumba zuwa ranar 5 ga watan, kuma babban magatakardan MDD Ban Ki-moon zai halarci taron bisa gayyatar da aka yi masa.
Ban Ki-moon ya nuna yabo matuka ga kasar Sin domin ta gayyaci shugabanni da manyan jami'an kasashe masu tasowa zuwa taron, kuma bisa labaran da aka samu, an ce, kasar Laos dake shugabancin kungiyar ASEAN a wannan karo, kasar Chadi dake shugabancin kungiyar AU a wannan karo, kasar Senegal dake shugabancin kungiyar abokantaka ta nahiyar Afirka a wannan karo, kasar Thailand dake shugabancin kungiyar G77 a wannan karo, za su halarci taron kolin G20, haka kuma kasashen Kazakhstan da Masar, manyan kasashe biyu masu tasowa za su halarci taron kolin G20 na Hangzhou, bisa gayyatar da kasar Sin ta yi musu.
Haka kuma, taron kolin da za a yi a wannan karo zai kasance taro mafi samun halartar kasashe masu tasowa cikin tarihin taron kungiyar G20. (Maryam)