in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A karon farko G20 za ta mayar da batun neman bunkasuwa a matsayin muhimmin batu cikin tsarin manufofin duniya
2016-08-26 20:24:14 cri

Sakamakon kokarin da kasar Sin ta yi, ya sa a karon farko kungiyar G20 za ta mayar da batun neman bunkasuwa a matsayin muhimmin batu cikin tsarin manufofin kasa da kasa a bana.

Mr. Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin shi ne ya bayyana hakan yau Jumma'a a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan birnin Beijing.

Lu Kang ya kara da cewa, kasar Sin za ta yi kira da a hada kai wajen goyon bayan raya masana'antun kasashen Afirka da kasashen da ba su ci gaba ba, a kokarin taimaka musu gaggauta raya masana'antunsu, ta yadda za su cimma burinsu na rage talauci da samun ci gaba mai dorewa.

Lu ya ci gaba da cewa, ya yi imani da cewa, yadda kungiyar G20 ke mayar da hankali kan batun bunkasuwa a yayin taron kolin Hangzhou zai kara taimakawa kasashen duniya cimma daidaito a kan batun, tare da sa kaimi kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China