Matakan kara inganta harkokin ciniki da zuba jari, a maimakon ba da kariya a harkokin ciniki da zuba jari, muhimmin batu ne da aka sake nanatawa da kuma cimma daidaito a kai a yayin tarukan koli da kungiyar G20 ta shirya a baya.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ne ya fadi hakan a yau Jumma'a yayin taron manema labaru da aka shirya a nan Beijing, inda ya ce, a yayin taron koli da za a gudanar a birnin Hangzhou na kasar Sin a farkon wata mai zuwa, za a kara mayar da hankali kan tsara shirin ayyuka na Hangzhou, wanda zai kasance a matsayin wani matakin da ya dace a dauka wajen raya tattalin arzikin duniya mai dorewa cikin daidaito kuma yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)