in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Batun Afirka zai zama daya daga cikin muhimman batutuwan da za a tattauna a yayin taron G20
2016-08-26 18:35:28 cri
A yau Jumma'a da safe, a yayin taron masana samari na kasa da kasa na G20 da aka shirya a nan Beijing, masana samari wadanda suka halarci taron sun tattaunawa tare da yin muhawara sosai bisa jigon "sa ido kan yadda kasar Sin ke taka rawa a aikin tafiyar da harkokin duniyarmu", kuma sun tabbatar da cewa, batun neman bunkasa Afirka zai zama daya daga cikin muhimman batutuwan da za a tattauna a yayin taron G20 da za a yi a birnin Hangzhou na kasar Sin a wata mai zuwa.

Mr. Liu Naiya, masani kan nazarin harkokin Afirka a cibiyar nazarin harkokin zaman al'umma ta kasar Sin ya ce, halin da kasashen Afirka suke ciki wajen neman ci gaba, musamman ci gaban masana'antu da sakamakon da suka samu za su zama muhimmin batun da zai jawo hankulan shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20. Bangaren Sin ya sanya batutuwan da suke shafar kasashen Afirka, kuma ya gayyaci wakilan wasu kasashen Afirka su halarci taron G20, wannan ya alamta cewa, kasar Sin tana kulawa sosai da batutuwan da suka shafi ci gaban kasashen Afirka. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China