in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara ba da gudunmawa wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya
2016-08-26 11:21:29 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya shaidawa manema labaru cewa, Sin za ta gudanar da aikin diplomasiyya masu tarin yawa tun daga farkon wata mai zuwa, don ganin ta karbi bakuncin taron koli na G20 cikin nasara, tare kuma da halartar wasu muhimman ayyuka na shiyya-shiyya da na kasa da kasa.

Mr. Wang Yi wanda ya bayyana hakan bayan ganawa da takwaransa na kasar Albania Ditmir Bushati a jiya Alhamis a nan birnin Beijing, ya kara da cewa Sin za ta yi amfani da wadannan tsare-tsare na hadin gwiwa, wajen kara ba da gudummawa a fannin sa kaimi ga zurfafa hadin gwiwa tsakanin shiyya-shiyya, da kyautata tsarin duniya.

Mista Wang ya ce taron koli na G20 ya kasance wani muhimmin aikin diplomasiyya a wannan shekara, kuma ya zama wani dandali na kyautata tsarin duniya, da ya jawo hankalin al'ummar duniya. Don haka Sin ta yi shiri yadda ya kamata na gudanar taron bisa taimakon da bangarori daban-daban suka bayar.

Ya ce yanzu birnin Hangzhou a shirye yake Sin kuma a shirye take. An yi imanin cewa, taro a wannan karo zai biya bukatun bangarori daban-daban kuma zai cimman nasara yadda ya kamata, tare da ba da gudunmawa wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da kyautata tsarin duniya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China