A yau ne a nan birnin Beijing aka kaddamar da wani rahoto dangane da kwarewar kasashe mambobin kungiyar G20 ta fuskar yin kirkire-kirkire.
Rahoton ya yi bayanin cewa, a cikin kasashe mambobin kungiyar G20, kasashen Amurka, Birtaniya da Japan su ne suke kan gaba ta fuskar yin kirkire-kirkire, yayin da kasar Sin take matsayi na 9, wadda ta zama kasa mai tasowa daya tilo daga cikin kasashe masu tasowa guda goma mafi kwarewa ta fuskar yin kirkire-kirkire, lamarin da ya nuna cewa, a shekarun da suka wuce, kasar Sin ta samu sakamako mai kyau wajen aiwatar da manufar raya kasa ta hanyar yin kirkire-kirkire, ta kyautata kwarewarta sosai ta fuskar kirkire-kirkire. (Tasallah Yuan)