in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da Rasha sun riga kawar da babbar matsalar da ta hana tsagaita bude wuta a Syria
2016-08-27 13:39:16 cri
Ministan harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya bayyana a daren jiya Jumma'a a birnin Geneva cewa, ban da wasu kananan matsaloli, kasar Amurka da kasar Rasha sun riga sun warware babbar matsalar da ta hana tsagaita bude wuta a kasar Syria.

A wannan rana, John Kerry ya zanta da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov kan batun kasar Syria har na tsawo awoyi guda 10.

Bayan zantawar tasu, Mr. Lavrov ya bayyana cewa, an samu babban ci gaba kan batutuwan dake shafar yadda za a tsagaita bude wuta a kasar Syria, da kuma tabbatar da ayyukan ba da agaji yadda ya kamata a kasar da dai sauransu, haka kuma, ana ganin cewa, zantawar da suka yi za ta taimaka wa kasashen Amurka da Rasha wajen karfafa fahimtar juna tsakaninsu kan batun Syria.

Bisa kudurin da kwamitin tsaron MDD ya yanke kan wannan batu, an ce, ya kamata bangarorin da rikicin kasar Syria ya shafa su kulla yarjejeniyar kawo sauyin siyasa a kasar Syria kafin ranar 1 ga watan Agusta na bana, amma, an yi ta bata yanayin tsaron kasar Syria bayan taron shawarwarin neman sulhu kan batun Syria zagaye na biyu da aka yi a birnin Geneva a ran 27 ga watan Afrilu na bana, lamarin da ya gurgunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kasar Amurka da kasar Rasha suka kulla a watan Fabrairu na bana, kuma har zuwa yanzu, an kasa tabbatar da lokacin gudanar da shawarwarin neman sulhu zagaye na uku. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China