in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu boma-bomai sun fashe a birnin Kameshli dake kasar Syria
2016-07-27 20:07:52 cri
A yau Laraba ne, wasu boma-bomai suka fashe a birnin Kameshli dake kudu maso gabashin kasar Syria, wadanda suka haddasa mutuwar mutane a kalla 31, yayin da mutane fiye da 100 suka ji rauni.

Rahotanni na cewa, bam na farko ya fashe ne a dab da wani sansanin dakarun Kurdawa, maharan sun kai hare-haren ta hanyar tuka wata mota shake da abubuwan fashewa a cikinta, kana bam na biyu kuma ya fashe ne a shingen duba ababan hawa na dakarun Kurdawa. Mutane da dama sun ji munanan raunuka, watakila yawan mutanen da suka mutu a sakamakon harin zai karu. Yanzu haka ana ci gaba da aikin nema da bada ceto ga mutanen da suka ji rauni.

Kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai harin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China