A wannan rana, mista Staffan de Mistura ya soke taron mako-mako na rukunin shigar da kayayakin jin kai cikin Syria a Geneva, da zummar jawo hankulan kasa da kasa kan yanayin da ake ciki a fannin jin kai a Syria, musamman ma a yankin Aleppo, wanda yake kara tsananta a kullum.
A ranar Talata ne, kwamitin cika aiki na kasa da kasa mai zaman kansa kan batun Syria da hukumar kula da hakkin bil'adam ta MDD ta dora alhaki ya bayyana cewa, a cikin makwannin da suka wuce, bangarorin da ke fada da juna a Syria sun sake gwabzawa a yankin Aleppo, lamarin da ya jefa fararen hula kimanin miliyan 2 cikin matsalar karancin abinci da ruwan sha.