in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu mutane sun mutu a sakamakon fashewar boma-boman hayaki mai guba a birnin Aleppo na kasar Syria
2016-08-03 10:47:07 cri

A jiya Talata ne aka kai wasu hare-hare da boma-boman masu guba a birnin Aleppo dake kudancin kasar Syria, hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 5, a yayin da wasu mutane 8 kuma suka jikkata.

Kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya ba da labari cewa, wasu dakaru sun kai farmaki a birnin Aleppo da ke karkashin ikon sojojin gwammatin kasar Syria, sannan kuma suka yi amfani da boma-bomai masu guba, lamarin da ya haddasa wasu mutanen fuskantar matsalar shakar numfashi.

Bugu da kari, wani hari da aka kaddamar a wannan rana ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2, kana wasu mutane 11 suka jikkata.

A baya dai maharan sun sha kai hare-hare a birnin na Aleppo wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar fararen hula a kalla 30, a yayin da mutane 210 kuma suka jikkata. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China