Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya bayar, an ce, za a nada Hammis a matsayin sabon firaministan kasar, don ya maye gurbin firaministan kasar mai ci yanzu Wael Nader al-Halqi. Ana kuma sa ran ba da jimawa ba za a gabatar da jerin sunayen sabbin ministoci.
Hammis ya zama ministan wutar lantarki na kasar a cikin gwamnatin al-Halqi.
An yi zaben majalisar dokokin jama'ar kasar Syria a ranar 13 ga watan Afrilu na bana. Sabuwar majalisar dokokin ta yi rantsuwar kama aiki a ranar 6 ga watan Yuni. Bisa dokokin kasar, ya kamata a kafa sabuwar majalisar ministocin kasar a cikin kwanaki 40 bayan rantsuwar kama aikin sabuwar majalisar dokokin kasar. (Zainab)