Rahotanni sun ce, wasu dakaru sun taba hana wadannan fararen hula ficewa daga yankin dake karkashin ikonsu, a daya bangare kuma, wasu dakaru sun mika wuya ga gwamnatin kasar.
A baya, gwamnatin kasar Syria ta bude manyan hanyoyi guda uku ga al'ummomin kasar domin janye su daga yankin dake karkashin mallakar dakaru na jam'iyyun adawa, haka kuma, gwamnatin ta yi alkawarin cewa, za ta kula da al'ummomin yadda ya kamata bayan sun fita daga yankin.
Birnin Aleppo ya taba kasance cibiyar tattalin arzikin kasar Syria, yayin da kuma birni mafi girma na wannan kasa. Amma, cikin dogon lokacin da suka gabata, sojojin gwamnatin kasar suna mallakar yammacin birnin, yayin da gabashin birnin ke karkashin mallakar dakaru na jam'iyyun adawa da kuma kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi.
Kana, a halin yanzu, sojojin gwamnatin kasar suna yin kawanya kan yankin dake karkashin mallakar dakarun, inda sojojin gwamnatin suka yi kira ga dakarun jam'iyyun adawa da su aje makamansu don mika wuya.
Kaza kila, shugaban kasar Syria Bashar al Assad ya samar da wani shirin nuna afuwa a ran 28 ga watan nan da muke ciki, inda ya sanar da yin afuwa ga dakarun da suka mika wuya ga gwamnati cikin watanni uku masu zuwa. (Maryam)