in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira da a inganta matakin warware batun Syria ta hanyar siyasa
2016-08-23 15:12:38 cri
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD mista Wu Haitao, ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen duniya su tsaya tsayin daka wajen warware kalubalen da kasar Syria ke fuskanta ta hanyar siyasa.

Mista Wu ya bayyana haka ne, a yayin taron da kwamitin sulhu na jiya Litinin wanda aka gudanar game da kasar ta Syria. A cewar sa a kwanan baya rikici ya kara tsananta a kasar Syria, yayin da yanayi ke kara tabarbarewa a yankin Aleppo. Don hake ne kasar Sin ke nuna matukar damuwa game da asarar rayukan fararen hula, da raunatar wasu masu yawa, da kuma halin jin kai da al'ummun kasar ta Syria ke ciki.

Mista Wu ya kara da cewa, a ko da yaushe kasar Sin na goyon bayan sassauta matsalar jin kai a Syria, kuma tana samar da taimakon jin kai ta hanyoyi daban daban ga kasar, da ma wasu kasashen dake yankin, ta hanyar samar da hatsi da sauran kayayyakin bukata.

A cewar mista Wu, warware batun Syria a siyasanci muhimmiyar hanya ce ta magance matsalolin da suka shafi kasar, ciki har da matsalar jin kai. Don haka ya kamata sassa daban daban a Syria su mai da hankali kan moriyar jama'ar kasar, su kuma halarci shawarwarin zaman lafiya na Geneva, don cimma wani shiri na warware batun da zai iya samun amincewa daga dukkanin bangarori. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China