in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na maraba da baki daga sassa daban daba na duniya
2016-08-24 20:18:27 cri

Kasar Sin ta ce ta shirya tsaf don karbar bakuncin taron kolin kungiyar G20, tana kuma maraba da baki daga sassa daban daban na duniya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ne, ya sanar da hakan a yau Laraba a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing.

Mista Lu ya ce, sakamakon kokarin da bangarori daban daban suke yi, ana sa ran cewa, za a samu sakamako mai kyau a fannoni kusan 30 a yayin taron kolin G20 da za a gudanar a birnin Hangzhou, lamarin da zai sanya taron kolin na Hangzhou zama taron koli mafi samun sakamako da yawa. Kasashe masu ruwa da tsaki suna fatan inganta hadin gwiwa wajen tabbatar da ganin, an gudanar da taron kolin na Hangzhou cikin nasara, wanda zai kara taimakawa wajen bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Rahotanni na nuna cewa, baya ga shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20, kasar Sin ta gayyaci shugabannin kasashen Chadi, Masar, Senegal da wasu kasashe masu tasowa da su halarci taron. Dangane da lamarin, mista Lu ya ce, ana sa ran kasashe masu tasowa da aka gayyata za su bayyana ra'ayoinsu a yayin taron kolin na Hangzhou. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China