in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Duniya ya shirya sayar da takardun bashi na SDR kafin bude taron kolin G20
2016-08-22 20:32:04 cri

Hukumar sa ido kan harkokin takardun hada-hadar kudi ta kasar Sin ta ruwaito Arunma Oteh, mataimakiyar shugaban Bankin Duniya kuma babbar jami'ar kula da jarin bankin tana cewa, Bankin Duniya ya shirya sayar da takardun bashi na kudaden ajiyar bankunan kasar Sin kafin bude taron kolin kungiyar kasashe ta G20 na bana.

Madam Oteh ta fadi haka ne yayin da take ganawa da mataimakin shugaban hukumar sa ido kan harkokin takardun hada-hadar kudi ta kasar Sin Fang Haixing a nan Beijing.

A nasa bangaren, mista Fang Haixing ya ce, ana maraba da Bankin Duniya da ya zuba jari a kasuwar jarin kasar Sin, lamarin da zai kara ba da gudummowa wajen ci gaban kasuwar. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China