in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kwace hauren giwa Kg.80 a Ruwanda
2016-08-21 13:22:39 cri
Rundunar 'yan sandan kasar Ruwanda ta gaskata cewa, a ranar 19 ga wannan wata, 'yan sandan kasar sun kwace hauren giwa mai nauyin kilogram 80, yayin da ta kama mutane 10 da take tuhuma da aikata laifuffukan da suka shafi safarar hauran giwayen.

Haka kuma, 'yan sanda sun bayyana cewa, cikin wadannan mutane 10 da suka kama, akwai 'yan kasar Ruwanda 6, yayin da 'yan kasar Guinea 4.

Bisa binciken farko da aka yi, an ce, sun yi fasa kwaurin wadannan hauren giwaye ne daga kasar Tanzania zuwa kasar Ruwanda, kuma 'yan fasa kwauri suna shirya jigilar wadannan hauren giwaye ne zuwa nahiyar Asiya.

A watan Maris na bana, koton Ruwanda ta yanke hukuncin daurin 6 a gidan kurkuku kan masu fasa kwaurin su 3 'yan kasar Guinea da kuma dan kasar Ruwanda 1, wadanda suka yi fasa kwaurin hauren giwaye mai nauyin kilogram 88. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China