Sanarwar da aka fitar bayan wani taron ministoci na gaggawa da shugaba Kagame ya jagoranta, ta nuna cewa, 'yan kasar Rwanda dake kasashen waje za su jefa kuri'a a ranar 17 ga watan Disamban shekarar 2015 a yayin da wadanda suke cikin kasa za su jefa a ranar 18 ga watan Disamba. Bisa tanade tanaden kundin tsarin mulki da sauran dokoki, shugaban jamhuriya ya ba da amincewarsa wajen shirya wani zaben raba gardama kan kundin tsarin mulkin da aka yi wa gyaren fuska a shekarar 2015 bisa ga na ranar 4 ga watan Yunin shekarar 2003, in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)