in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Rwanda ta koma CEEAC
2016-08-19 13:32:01 cri
Ministan harakokin wajen Rwanda, madam Louise Mushikiwabo ta mikawa sakatare janar na kungiyar hadin kan kasashen Tsakiyar Afrika (CEEAC),mista Ahmad Allami-Mi, da wata wasikar kasarta domin sake komawa cikin kungiyar a ranar jiya Alhmis a birnin Libreville.

Shugabar diplomasiyyar Rwanda ta bayyana cewa, ta zo da sunan kasar domin komawa cikin kungiyar CEEAC dindin. Tun a cikin watan Mayu ne na shekarar 2015 kasar take fadi tashin ganin ta koma kungiyar CEEAC.

Madam Mushikiwabo ta nuna farin cikin dawowar kasarta a cikin kungiyar, inda ta shaida cewa CEEAC, kungiya ce mai mahimmancin gaske. Tun bayan yakin basasan da ya barke a kasar a shekarar 1994, Rwanda ta mai da hankali kan inganta harkokin tattalin arzikinta.

Jami'ar ta kara da cewa kasar kuma mamba ce ta kungiyar kasashen gabashin Afrika, kuma tun tuni ta amince da kasancewa mamba ta kungiyoyin kasashen gabashin Afrika da ta tsakiyar kasashen Afrika.

A cewar shugabar diplomasiyar Rwanda, kasar a shirye take domin taka rawar gani an samu ci gaban kungiyar CEEAC.

Rwanda ta kasance kasa ta goma sha daya ta kungiyar, kuma ita ce kasa ta farko a cikin CEEAC mai amfani da harshen Turanci. Kasashen goma sha daya na CEEAC sun hada da Angola, Burundi, Kamaru, Afrika ta tsakiya, Kongo, Gabon, Guine Ekatoriale, Jamhuriyar Demokradiyar Kongo (RDC), Rwanda, Tchad, da SaoTome et Principe. (Laouali Souleymane)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China