in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ruwanda zai sake yin takara a babban zaben shugaban kasar a shekarar 2017
2016-01-03 14:09:20 cri
A ran 1 ga wata, shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya sanar da cewa, bisa sakamakon jefa kuri'u game da gyaran kundin tsarin mulkin kasar da aka yi a karshen shekarar da ta wuce, zai sake shiga babban zaben shugaban kasa da za a yi a shekarar 2017 bayan da ya kammala wa'adin aikinsa na biyu na shekaru 7 kan ragamar mulkin kasar.

A ran 18 ga watan Disamba na shekarar 2015, an kada kuri'u kan gyaran kundin tsarin mulkin kasar Ruwanda, inda aka amince da rage wa'adin aikin shugaban kasar daga shekaru 7 zuwa shekaru 5, kuma sau daya kawai shugaban kasar zai ko za ta iya sake lashe babban zaben shugaban kasar. Kana, kafin a aiwatar da sabon kundin tsarin mulkin kasar, an kafa lokacin sauyin siyasa na shekaru 7, a lokacin kuma, dukkanin 'yan takara, har ma da Paul Kagame za su iya shiga babban zaben shugaban kasar. Lamarin da ya nuna cewa, idan Paul Kagame zai iya sake lashe babban zaben, to zai iya ci gaba da kasancewa kan ragamar mulkin kasar har zuwa shekarar 2024.

Daga bisani kuma, bisa sabon kundin tsarin mulkin kasa da za a iya fara yin amfani da shi a shekarar 2024, Paul Kagame zai kuma sami damar halatar babban zaben shugaban kasar har sau biyu, lamarin da zai iya ba shi dama tsawaita wa'adin aikinsa zuwa shekarar 2034, idan zai iya cimma dukkan zababbun da za a yi a nan gaba.

Bisa tsarin mulkin kasar Ruwanda na yanzu, an ce, wa'adin aikin shugaban kasar shekaru 7 ne, kuma sau biyu shugaban kasar zai iya kasance kan ragamar mulkin kasa, a shekarar 2003 da ta 2010, sau biyu Paul Kagame ya lashe babban zaben shugaban kasar, shi ya sa, bisa tsarin mulkin kasar da ake amfani da shi a kasar Ruwanda a halin yanzu, Paul Kagame ba zai iya halarci babban zabe karo na uku ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China