in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta gudanar da taron manema labari game da taron koli na 11 na shugabannin kungiyar G20
2016-08-15 18:49:01 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta gudanar da taron manema labaru a yau Litinin, inda mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Baodong, da sauran jami'ai suka yi bayani game da yanayin taron koli na 11 na shugabannin kungiyar G20, wanda shugaban kasar Sin zai halarta, tare da sauran bukukuwan da zai halarta a lokacin taro. Kana sun amsa tambayoyin da 'yan jarida suka gabatar musu.

Cikin jawabin sa, Mr. Li Baodong ya bayyana cewa, tun daga ranar 4 zuwa 5 ga watan Satumba mai zuwa, za a gudanar da taron koli na 11 na shugabannin kungiyar G20 a birnin Hanzhou na nan kasar Sin, inda shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta G20, da shugabannin kasashen da aka gayyata, da kuma shugabannin hukumomin kasa da kasa za su halarci taron.

Ya ce a yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai tattauna tare da bangarori daban daban kan manyan batutuwa. Kaza lika kafin taron, shugaba Xi zai halarci bikin bude taron koli na masana'antu, da cinikayya na kungiyar G20 inda zai gabatar da jawabi, tare da bayyana ra'ayoyi game da tattalin arzikin Sin, da na duniya, da kuma sarrafa tattalin arzikin duniya. Kamar yadda aka saba, shugabannin kasashe membobin kungiyar BRICS za su yi kwarya-kwaryar ganawa, inda shugaba Xi Jinping zai halarci taron da kuma yi jawabi.

A yayin taron kolin kuwa, Xi Jinping zai gana da shugabannin wasu kasashe, don yin musayar ra'ayoyi game da batutuwan taron kolin, da dangantakar Sin da sauran kasashen, da kuma batutuwan kasa da kasa da na yankuna. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China