Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya sanar a yau Litinin 15 ga wata cewa, za a kira taron koli zagaye na 11 na shugabannin kungiyar G20 a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin daga ran 4 zuwa 5 ga watan Satumban bana. Taken taron shi ne "Shimfida yanayin tattalin arzikin duniya mai kirkire-kirkire, kuzari, da hadin gwiwa". Shugabannin kasashe membobin kungiyar ta G20 da shugabannin kasashen da aka gayyata da kuma jami'an kungiyoyin kasa da kasa masu ruwa da tsaki ne za su halarci taron. Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarta tare da jagorantar taron, haka kuma zai halaraci kwarya-kwaryar taron shugabanin BRICS da sauran harkoki.
Rahotanni na cewa, za a kira taron koli na masana'antu da kasuwanci na kungiyar G20 daga ran 3 zuwa 4 a watan Satumba a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang da ke nan kasar Sin, inda kuma shguaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude taron tare da yin jawabi. Ana sa ran wasu shugabannin kungiyar G20 da bakin da aka gayyata da sauran shugabannin kungiyoyin kasa da kasa masu ruwa da tsaki za su halarci taron. (Amina)