Kafin bude taron koli karo na 11 na G20 a birnin Hangzhou na kasar Sin, mataimakin babban direkta janar na kungiyar WTO Yi Xiaozhun ya bayyana cewa, a lokacin da ake fuskantar rashin bunkasuwar tattalin arziki da cinikayya a duniya, idan shugabannin kasashe daban daban za su tattaunawa kan batun cinikayya da zuba jari a gun taron koli na G20 da kuma tabbatar da sakamakon da aka samu a gun taron ministocin cinikayya na G20, to hakan zai taka rawa sosai wajen bunkasa cinikayya cikin dogon lokaci a nan gaba.
Mr. Yi Xiaozhun yana ganin cewa, a matsayin kasa mai masaukin baki na wannan taron kolin G20, kasar Sin tana dora muhimmanci sosai kan batun cinikayya da zuba jari kamar yadda ta yi a kan batutuwan harkokin kudi da manufar hada-hadar kudi, kuma wannan kudurin da Sin ta dauka bisa daidaici da kuma muhimmanci sosai. (Lami)