Masana daga nahiyar Afirka sun bayyana kyakkyawar fatansu na cewa, taron kolin G20 da za a gudanar a birnin Hangzhou na kasar Sin a watan Satumba, zai magance manyan matsalolin da ke ci wa duniya tuwa a kwarya, musamman kasashe masu tasowa.
Wani mai bincike kan harkokin raya kasa a jami'ar kasar Afirka ta Kudu Sabelo Gatsheni-Ndlovu ne ya bayyana hakan cikin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin. Yana mai cewa, bai kamata taron kolin na G20 ya yi watsi da matsalar muhalli, ta'addanci, da harkokin ci gaba da duniya take fuskanta ba.
A cewar masanin, kamata ya yi a bullo da matakan da suka dace na magance matsalar rashin ci gaba da matsalar canjin yanayi da duniya take fuskanta, maimakon yadda kasashen da suka ci gaba suke ta bata lokaci suna ta zargin juna.
Da ya juna ga barazanar ta'addanci kuwa, Gatsheni-Ndlovu ya jaddada muhimmancin hukunta wadanda suke samar da makamai ga 'yan ta'adda. Ya kuma zargi wasu kasashen yamma da rura wutar tashin hankali, ta hanyar goyon bayan wasu kungiyoyin 'yan ta'adda a kasashe kamar Jamhuriyar demokiradiyar Congo, Iraki, Syria da wasu kasashen Afirka.
Bayanai na nuna cewa, a yayin taron kolin na G20, ana sa ran kasar Afirka ta Kudu za ta gabatar da wasu batutuwan da ke damun Afirka da kasashe masu tasowa kamar yadda manufofinta na kasashen waje suka tanada.(Ibrahim).