A yayin da aka shiga yini na uku a gasar wasannin Olympics da ke gudana yanzu haka a birnin Rio na kasar Brazil, kasar Sin ta kara lashe lambobin zinare a wasannin linkaya da tsallen fadawa ruwa.
Sun Yang ya lashe lambar zinare a wasan linkaya na mita 200 cikin minti 1 da dakika 44.65, kuma wannan ita ce lambar zinare na farko da kasar Sin ta lashe a wannan gasa, kana lambar zinare ta uku da ya lashe a gasar ta Olylmpics.
A bangare guda kuma Lin Yue da Chen Aisen suma sun lashe lambar zinare a wasan tsallen fadawa cikin ruwa bangaren maza. Sakamakon da ke nuna cewa, kawo yanzu kasar Sin ta lashe lambobin zinare a dukkan wasannin tsallen fadawa ruwa a gasar wasannin Olympics na wannan karo.(Ibrahim)