in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar wakilan 'yan gudun hijira ta halarci bikin bude gasar Olympics
2016-08-06 13:11:06 cri
A ranar 5 ga watan Agusta da dare, an yi bikin bude gasar wasannin Olympics na yanayin zafi karo na 31 a birnin Rio de Janeiro dake kasar Brazil, kuma wannan shi ne karo na farko da aka bude gasar Olympics a nahiyar Amurka ta Kudu.

Za a fara gasar wasanni tun daga ranar 6 ga wata, sa'an nan za a kawo karshen gasar a ranar 21 ga watan nan da muke ciki.

Bugu da kari, wata tawagar wakilan Olympics ta 'yan gudun hijira ta halarci bikin bude gasar da aka yi a daren jiya, wadda ta kasance tawagar wakilan 'yan gudun hijira ta farko da ta halarci bikin bude wasannin Olympics cikin tarihi.

Haka kuma, dangane da wannan harka, hukumar 'yan gudun hijira ta MDD ta fidda wata sanarwa a ran 5 ga wata cewa, ta taya wa tawagar 'yan gudun hijirar din murnar na halartar bikin da kuma shiga gasar wasannin da za a yi, sa'an nan ta bayyana cewa, an kafa tawagar wakilan Olympics ta 'yan gudun hijira domin janyo hankulan al'ummomin kasa da kasa kan batun 'yan gudun hijira, sabo da a halin yanzu, akwai mutane kimanin miliyan 65.3 da su bar kasashensu sakamakon rikice-rikice da tashe-tashen hankulan da aka yi a wurare daban daban na duniya. Shi ya sa, wakilan 'yan gudun hijira suna son nuna aniya da kuma fatansu ga kasa da kasa ta hanyar halartar babbar gasar kasa da kasa ta wasannin Olympics. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China