Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na Rio Carlos Arthur Nuzman ya bayyana cewa, mun shirya sosai don kafa sabon tarihi. Kasar Brazil ta fuskanci matsaloli da dama a fannonin siyasa da tattalin arziki a lokacin da take shirye-shiryen daukar bakuncin gasar, amma duk da haka mun yi kokarin kammala ayyuka daban-daban, kuma za mu iya gudanar da wannan gasa cikin nasara.
Zakaran wasan takobi na maza a gasar Olympics ta London Lei Sheng, shi ne zai rike tutar tawagar kasar Sin a gasar mai mutane 711 da za ta halarci bikin bude gasar Olympics. 'Yan wasan kasar Sin 416 ne za su fafata a gasar, adadi mafi yawa a cikin tarihin gasar ta Olympics. Ana saran za su shiga manyan wasanni 26, da kuma kananan wsanni 210. Kamar kullum ana fatan, 'yan wasan kasar Sin za su yi kokarin lashe lambobin yabo na zinariya a wasannin kwallon tebur da wasan badminton da tsunduma cikin ruwa da wasan daga nauyi da kuma harbi.
A ranar 21 ga watan Agusta ne, ake fatan kammala gasar wasannin Olympics ta Rio.(Lami)