A yayin da a jiya Laraba aka shiga rana ta biyar a gasar wasannin Olympics da ke gudana a Rio na kasar Brazil. 'Yan wasannin daga nauyi da kwallon tebur na kasar Sin ajin mata sun kara lashe lambobin zinare biyu. Yanzu haka kasar Sin ce ta ke matsayi na biyu da lambobin zinare 10, zurfa 5, da kuma tagulla 8.
Ya zuwa jiya Laraba da dare, kasar Amurka ce ta ke kan gaba da lambobin zinare 11, zurfa 11, da kuma tagulla 10, Sai kasar Japan wadda dauki matsayi na 3da lambobin zinare 6.(Lami)