in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Syria ta yi Allah wadai da rundunonin sojan ketare da su shiga kasar ba tare da samun izni ba
2016-06-16 10:43:16 cri
A jiya Laraba 15 ga wata, ma'aikatar harkokin waje ta Syria ta ba da sanarwa, inda da babbar murya ce ta yi Allah wadai da rundunonin sojan musamman na ketare da suka shiga arewacin kasar ba tare da samun izni ba.

A wannan rana kamfanin dillancin labaru na gwamnatin kasar ya yi amfani da sanawar ma'aikatar harkokin wajen kasar cewa, a cikin 'yan kwanakin da suka wuce, an ba da labarin cewa, rundunar sojan musamman na Faransa da na Jamus sun shiga yankin Ayn al-Arab da sauransu dake arewacin kasar, game da wannan batu, Syria ta yi Allah wadai da babbar murya. Kuma tana ganin cewa, wannan lamari ne da ya keta kundin tsarin mulkin MDD da kasancewa barazana ga ikon mallakar kasar Syria. Sanarwar ta ce, dole ne a yi hadin gwiwa da gwamnatin Syria domin gudanar da aikin yaki da ta'addanci bisa doka.

Daga bisani, ma'aikatar tsaron kasar Jamus ta musunta tura sojoji zuwa Syria. A ranar 9 ga wata, kafofin yada labaru na Faransa sun yi amfani da maganar wani jami'in gwamnatin Faransa cewa, rundunar sojan Faransa ta daukin nauyin ba da shawara kan aikin soja a cikin hadaddiyar kungiyar "Syrian Democratic Forces" mai adawa da gwamnati, domin ba da taimako wajen yaki da kungiyar IS.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China