in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Congo (Brazzaville) ta yi bikin cika shekaru 56 da samun 'yanci
2016-08-16 11:14:49 cri

A yayin bikin tunawa da cika shekaru 56 da samun 'yanci kan Congo (Brazzaville), an gudanar da jerin gwano da faretin sojoji a garin Madingou a gaban idon shugaban kasar Denis Sassou N'Guesso jiya Litinin 15 ga wata, da kuma wasu shugabannin kasashen Afrika biyar wadanda suka hada da Faustin Archange Touadera na Jamhuriyar Africa ta Tsakiya, Obiang Nguema Mbasogo na Guinee Equatorial, Hage Geingop na Namibiya, Alpha Conde na Guinee da Patrice Talon na Benin.

Al'ummar kasar da suka fito daga sassa 12 na kasar sun halarci bikin bisa tushen hada kan 'yan kasar baki daya.

Tun daga shekarar 2004 da ta gabata, gwamnatin Congo (Brazzaville) ta kaddamar da shirin raya ababen more rayuwa jama'a domin tunawa da samun 'yanci kan wannan kasa .(Laouali Souleymane).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China