A game da gyaran fuska ga tsarin mulkin kasar kuma Ban Ki-Moon, ya yi kira ga bangarorin daban-daban na kasar da su warware batun cikin lumana sannan har ila yau a cikin sanarwar, Magatakardar na MDD ya yi kira ga bangarorin daban-daban da su yin shawarwari kafin jefa kuri'ar raba gardama.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, game da soke ka'idojin dake shafar wa'adin tazarcen shugaban kasar a cikin sabon tsarin mulkin kasar, bangaren adawa na kasar Kongo(Brazzaville)da magoya bayansa sun yi zanga-zanga a birnin Brazzaville kwanan baya, don nuna adawa akan hakan.abinda ya kawo tashe-tashen hankali tare da yin sanadiyyar mutuwar mutane da jikkatar wasu da dama.(Bako)