in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Congo Brazzaville: 'Yan adawa sun kafa wani sabon kawance domin kare kundin tsarin mulkin kasar na yanzu
2015-08-02 13:02:52 cri
'Yan adawar kasar Congo Brazzaville sun sanar a ranar Asabar da kafa wani sabon kawancen siyasa, da suna ma taken "dubara domin demokaradiyya a kasar Congo Brazzaville" (IDC) da ke da manufar kare kundin tsarin mulkin kasar na ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2002. Sabon kawancen ya hada jam'iyyun siyasa, kungiyoyin jama'a, kungiyoyin fararen hula da suka lashi takobin kare kundin tsarin mulkin kasar dake aiki a yanzu haka domin karfafa zaman lafiya, demokaradiyya da kasa mai 'yanci, da kuma yaki da rashin aldaci daga dukkan fannoni tare da yin aiki domin samar da wata al'umma mai cike da gaskiya, ba wai mai nuna bambanci ba, in ji Serge Blanchard, daya daga cikin mambobin da suka kafa kawancen. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China