in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta rage yawan bashin da take bin Amurka
2016-08-16 10:50:02 cri

Alkaluman baya-bayan nan da sashen baitulmalin kasar Amurka ya fitar a jiya Litinin 15 ga wata ya nuna cewa, kasar Sin wadda ke kan gaba wajen baiwa kasar ta Amurka bashi, ta rage yawan bashin da ta baiwa Amurka a watan Yunin wannan shekara.

Bayanai na nuna cewa, a watan Yuni kasar Sin ta rage yawan bashin da ya kai kimanin dala biliyan 3.2, inda ya zuwa karshen watan Yuni ta bi Amurkar bashin da ya kai dala biliyan 1240.8.

Sai dai kuma a watan Mayu kasar ta Sin ta kara baiwa Amurka bashin dala biliyan 1.2 amma kuma yawan bashin da take bin Amurkan ya ragu a watannin Afrilu da kuma Maris.

Kasar Japan wadda ta kasance ta kasa ta biyu da ke bin Amurka bashi, ita ma ta kara baiwa Amurkar bashin dala biliyan 14.5 a watan Yuni, adadin da ya tasamma dala biliyan 1147.7.

Ya zuwa karshen watan Yuni, adadin basussukan ketare da ake bin Amurka ya karu daga dala biliyan 6209.9 a watan Mayu zuwa dala biliyan 6281. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China