An nada Theresa May a matsayin shugabar jam'iyya mai bin manufar ra'ayin rikau a hukumance
A jiya Litinin 11 ga wata, bayan janye jiki da dan takara Andrea Leadsom ya yi a zaben, shugaban jam'iyyar kwamitin 1922 mai bin manufar ra'ayin rikau ta Birtaniya, Graham Brady ya nada madam Theresa May a matsayin sabuwar shugabar jam'iyyar a hukumance. Daga bisani, David Cameron ya ba da sanarwa a fadarsa dake titin Downing mai lamba 10 cewa, zai mika duk ayyuka gare ta tun da wuri. An kiyasta cewa, madam Theresa May za ta hau kujerar firaministar kasar a hukunce kafin daren ranar Laraba ta wannan mako.(Fatima)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku