in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zambiya Edgar Lungu ya yi tazarce
2016-08-16 10:05:35 cri

Alkaluman karshe da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Zambiya ta bayar a jiya Litinin 15 ga wata, sun nuna cewa shugaba mai ci yanzu na kasar Edgar Lungu ya samu nasarar yin tazarce.

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, a cikin babban zaben da aka gudanar a ranar 11 ga wata, Edgar Lungu ya sami kuri'u kimanin miliyan 1.86, wanda ya kai kashi 50.35 cikin dari, yayin da babban abokin takararsa na jam'iyyar UPND, Hakainde Hichilema ya sami kuri'u kimanin miliyan 1.76.

Bisa tanade tanaden sabon kundin tsarin mulkin kasar da ya fara aiki a watan Janairun bana, an ce, dan takarar shugaban kasa ba zai yi nasara ba sai dai ya sami kuri'u sama da kashi 50 cikin dari. Idan babu wanda ya yi nasara a zagaye na farko, 'yan takarar dake kan matsayi na farko da na biyu za su ci gaba da yin takara a zagaye na biyu bayan kwanaki 21.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China