Kimanin shugabannin jam'iyyun siyasar kasar 18 ne suka gudanar da taron tattaunawar zaman lafiyar, da shugabannin coci suka shirya a ranar 30 ga watan Maris da nufin kawo karshen tashin hankali da samar da zaman lafiya a lokutan gangamin yankin neman zabe, a zaben kasar da za'a gudanar a ranar 11 ga watan Augustan wannan shekara.
To sai dai jamiyyar Patriotic Front (PF) mai mulki ta zargi babbar jam'iyyar adawa ta (UPND) da yin watsi da waccan yarjejeniya da aka amince da ita ta hanyar kitsa tashe tashen hankula.
Frank Bwalya, mataimakin mai Magana da yawun jam'iyyar PF mai mulki ya ce, a bayyane take karara cewa, shugabannin jamiyyar adawar basa yin gargadi ga magoya bayan su, bisa la'akari da yadda magoya bayan na su ke amfani da muggan kalamai ga abokan hamayyarsu.
Bwalya ya shedawa 'yan jaridu cewa jama'ar Zambiya da dama sun ji irin kalaman da shugabannin jam'iyyar UPND ke yiwa ga PF game da yarjejeniyar zaman lafiyar.
A ranar Lahadi ne dai magoya bayan UPND suka lalata ofishin jamiyyar mai mulki a Lusaka, domin huce haushi kan magoya bayan jamiyyar mai mulki.