Shugaban na Zambiya ya bayyana cewar ya cika alkawarin da ya daukawa al'ummar kasar a lokacin da yake rantsuwar kama aiki a ranar 25 ga watan Janairu, inda ya sha alwashin samarwa kasar sabon kundin tsarin mulki kafin babban zaben kasar a shekarar 2016.
A jawabin da ya gabatar a gaban daruruwan al'ummar kasar a babban dandalin taron kasar dake Lusaka babban birnin kasar, shugaba Lungu, ya bayyana cewar aikin samar da kundin tsarin mulkin kasar ba karamin al'amari ba ne, amma ya ce, Zambiya da al'ummar kasar ba za su taba mantawa da wannan rana ba, saboda a cikin ta ne aka kaddamar da kundin tsarin mulkin kasar wanda ya shafi muradu na jama'ar kasar tun bayan samun 'yancin kasar a shekarar 1964.
A watan Disambar shekarar da ta gabata ne, majalisar dokokin kasar ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar.
Shugban na Zambiya ya ce, yana fatan gyaran da aka yi ga kundin tsarin mulkin kasar zai haifar da hadin kan kasa da ci gaban al'umma, kasancewar batutuwan dake kunshe cikinsa sun shafi muradun dukkannin al'ummomi dabam dabam na jama'ar kasar ne.(Ahmad Fagam)