in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zhang Dejiang ya kai ziyara a kasar Zambia
2016-03-23 11:21:20 cri

Bisa gayyatar da shugaban majalisar dokokin jama'ar kasar Zambiya Patrick Matibini ya yi masa, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang ya kai ziyara a kasar Zambiya tun daga ranar 18 zuwa 22 ga wata, inda ya gana da shugaban kasar Lungu, tare da yin shawarwari da kuma ganawa da shugaba na farko na kasar Zambiya Kenneth David Kaunda.

Yayin da yake ganawa da shugaba Lungu, Zhang ya isar da sakon gaisuwa daga shugaban kasar Sin Xi Jinping. Zhang Dejiang ya bayyana cewa, kasar Zambiya kasa ce ta farko da ta kulla dangantakar diplomasiyya da kasar Sin a yankin kudancin nahiyar Afirka. Kasashen biyu sun sada zumunta da yin hadin gwiwa yadda ya kamata. A watan Disamba na bara, shugaba Xi ya gabatar da shirye-shirye 10 na hadin gwiwa tare da kasashen Afirka nan da shekaru 3 masu zuwa a gun taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC a birnin Johannesburg dake Afirka ta Kudu, inda ya bayyana imanin kasar Sin na nuna goyon baya ga kasashen Afirka da samun bunkasuwa mai dorewa. Kana ya yi fatan Sin da Zambiya za su kara yin hadin gwiwa kan ayyukan da aka tsara a gun taron koli da raya dangantakarsu yadda ya kamata.

Shugaba Lungu ya amince da shawarwarin da Zhang Dejiang ya gabatar game da aiwatar da ayyukan da aka tsara a gun taron koli na FOCAC. Kasar Zambiya ta dora muhimmanci sosai kan raya dangankatar dake tsakaninta da kasar Sin, yana fatan za a kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin samar da kayyayaki, hakar ma'adinai, da aikin noma da dai sauransu. Kana yana fatan kamfanonin Sin za su kara zuba jari da yin aiki a kasar Zambia.

Yayin da yake yin shawarwari tare da Matibini, Zhang Dejiang ya bayyana cewa, hukumar kafa dokoki muhimmin kashi ne na harkokin wata kasa, yana fatan za a kara yin hadin gwiwa da samar da gudummawa wajen inganta huldar dake tsakanin Sin da Zambiya ta hanyar ziyarar.

Yayin da yake ganawa da Kaunda, Zhang Dejing ya nuna yabo gare shi domin ya kiyaye yin kokarin sada zumunta a tsakanin Sin da Zambiya a lokacin da yake kan mukamin shugaban kasar Zambiya.

Kaunda ya waiwayi tarihin yin mu'amala tare da shugabannin kasar Sin a baya. Ya ce, jama'ar kasashen biyu sun yi hadin gwiwa, da samun nasarori kan inganta dangantakar dake tsakaninsu. Kasar Zambiya ta nuna godiya ga kasar Sin domin ta samar da gudummawa ga Zambiya wajen samun bunkasuwa, shi yana son ci gaba da nuna goyon baya ga sha'anin sada zumunta a tsakanin Sin da Zambiya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China