Mr Lungu wanda ya jagoranci bikin ya ce, yana son a tuna da shi a matsayin shugaban kasar da ya aiwatar da abin da ya fadi wajen yaki da cin hanci ta tabbatar da ganin cewa bai soma baki a cikin ayyukan hukumomin gwamnati ba wadanda ke da nauyin wannan aikin.
Mr Lungu ya kuma yi bayanin cewa, ba zai kare ko wane ma'aikacin gwamnati ba idan aka kama shi da laifin cin hanci, kuma ya ya yi gargadi dukkan masu rike da mukamai a gwamantin shi da 'yan kwangila wadanda suka saba kwashe kayayyakin da aka yi domin al'umma domin amfanin kansu da su guji ranar da hukunci zai hau kansu.
Gwamnati, in ji shi, har yanzu a tsaye take wajen ganin ta inganta hukumomin da suke ayyukan dakile cin hanci domin a samun nasarar kawo karshen shi gaba daya. A don haka ya shawarci hukumomi da kada su yarda wadansu mutane su yi amfani da su domin cimma nasu bukatun.(Fatimah)