Al'ummar kasar Zambia, sun fara kada kuri'u a babban zaben kasar, da kuma zaben raba gardamar gyaran kundin mulkin kasar. An dai bude runfunan zaben kasar ne da misalin karfe 6 na safiyar Alhamis din nan. Ana kuma sa ran 'yan kasar miliyan 6.7 ne za su jefa kuri'u, a rumfuna 7,700 dake sassan kasar daban daban.
Zaben na wannan karo ya kunshi na shugaban kasa, da 'yan majalissun dokoki 156, da wakilan kananan hukumomi 1,624, da na magajin garin yankuna, baya ga na raba gardama kan kwaskwarimar da ake fatan yiwa kundin mulkin kasar.(Saminu Alhassan)